nowayobloggers

Lafiya Uwar Jiki: Shan Zobo Na Rigakafin Cutar Hawan Jini - Bincike
( Daga Ahmed Abdullahi )

Sakamakon wani bincike da wani kwararre a cibiyar binciken Harkokin masana’antu da ke Oshodi jihar Legas, Dakta Ochuko Erukainure ya gudanar a kan ganyen Zobo ya tabbatar da cewa ruwan Zobo na da matukar tasiri wajen Rigakafin hawan jini.
Binciken ya nuna cewa ganyen Zobo ya kunshi sinadarin citric acid, Malevich acid da kuma tartaric acid wadanda ke taimakawa wajen Rigakafin Cututtukan suga da hawan jini.
Da yake karin haske game da binciken, Dakta Ochuko ya ce yana da muhimmanci a rika shan ruwa Zobo a duk lokacin da aka kammala cin abinci ba tare da sanya masa sikari ba don ganin ba a gurbata sinadiran da ke cikinsa.
Ya ce bin wannan tsari na shan Zobo yana taimaka wa wajen rage kiba, sanyi da. Wasu Cututtuka. Sai dai kuma kwararren ya yi gargadin cewa shan Zobo ga mai juna biyu(Ciki) yana da hadari saboda yana iya zubar da jikin .Ya ci gaba da cewa zobon zai iya haifar da zazzabin da jan ido ga mai juna biyu amma ya nuna cewa duk da yake babu wata shaida kan illar shan Zobo ga mai shayarwa, ya ba bada shawarar kaurace masa.

SHARE

Comments

    NO COMMENT

Leave Your Comment

Sign up to continue.

Your email address will not be published. Required fields are marked.

Already a member?? Login