nowayobloggers

Wasu Jami’o’I a tarayyar Najeriya sun fara nuna halin ko’in kula kan matakan da hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi da sauran manyan makarantu ta kasar,JAMB ta gindaya, kan rage makin samun gurbin karatu ga dalibai zuwa maki 120 ga mai neman jami’a da kuma 100 ga sauran manyan makarantu.Jami’ar tarayya ta Gusau a jihar Zamfara da ke arewacin kasar ta sanarda cewa sai dalibi ya samu maki 170 neza ta bashi gurbin karatu sabanin 120 da hukumar ta JAMB ta kayyade a baya-bayan nan.
A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasar, Jami’in yada labaran makarantar Malam Umar Usman ya ce jami’ar ta tsaida matakin ne la’akari da yawan daliban da suka nemi gurbin karatun, wanda kuma idan har ta amince da umarnin hukumar JAMB to fa bata da gurbin da zata debi ilahirin daliban.
Malam Umar Usman ya kara da cewa sama da dalibai 5000 ne yanzu haka kedakon gurbin karatu, kuma gurbin dalibai dubu 1 da dari biyar kadai take da shi.
A cewar sa idan da za a agazawa jami’ar da abubuwan da take bukata babu shakka zata iya daukar dalibai fiye da yadda take dauka a yanzu.
Dama dai tun bayan sanar da matakin hukumar ta JAMB kan adadin makin da jami’o’in za su rika bai wa dalibai gurbin karatu da shi, an yi ta samun kace nace daga bangarorin jami’o’in daiyaye dama sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilmi a Najeriyar.

SHARE

Comments

    NO COMMENT

Leave Your Comment

Sign up to continue.

Your email address will not be published. Required fields are marked.

Already a member?? Login