nowayobloggers

Gwamnatin tarayya karkashin hukumar nan mai kula da ilimin bai daya ta UBEC za ta samar da littattafan a dukkanin makarantun firamare na kasa a watan shida na wannan shekara ta 2017.
Babban sakataren hukumar UBEC na kasa Dakta Hamid Boboyi, shine ya tabbatar da haka, inda yake cewa, gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta himmatu wurin inganta harkan ilimi a kasar nan.
Hausa Online ta tattaro cewa Dakta Boboyi ya ce ba wai kawai littattafan lissafi da na turanci ba ne kawai gwamnatin za ta raba dukkanin darussan da ake koyarwa a matakin farko, kuma za a raba a dukkanin makarantun gwamnati dake kasar nan.
A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar jigawa ta ware kadadar noma 500 domin noman shinkafa ga matasan garuruwan Kwangwara da Bakin Kuja da Giwa da kuma Jangargari a yankin karamar hukumar Birnin Kudu.
Mataimaki na musamman ga gwamna kan noman shinkafa Alhaji Jamilu Dan Malam Jahun ya sanar da hakan a lokacin tantance matasan.
Ya ce gwamnatin jiha ta yi harrow a filin tare da haka rijiyoyi yayinda ake sa ran bada injinan ban ruwa da irin shinkafa da takin zamani da matasan zasu biya bayan girbin shinkafar.

SHARE

Comments

    NO COMMENT

Leave Your Comment

Sign up to continue.

Your email address will not be published. Required fields are marked.

Already a member?? Login