nowayobloggers

An yi wani mutum mai suna Bello a garin Dauran sokoto, mai aminchi da kaunan fadin gaskiya ko da zai kai ga mutuwa. Sabo da wannan hali ne ya zama sanan ne kwarai da gaske acikin garin. Wannan ya zama sanadiyan haddasa gaba a sakanin sa da wadanda basa jindadin kyawawan halayensa. Sai watarana daga cikin abokanen gabansa suka kunla masa makarkaciya domin su kashe shi, sai sukayi amfani da yaronsa maras jingari, ga shaye shaye, ga dauke dauke. Watarana, yaron malam Bello yaje yayi sata, labari kwa ya kai wurin malam Bello. Da jin haka sai yayi wa yaron mugun duka kwairai. A wannan rana ne abokanen gabansa suka je suka kama yaron, suka kasheshi,suka kuma kawo gawansa gida aboye domin mutane su tuhumeshi da laifin kisan kai. Amma sabo da ansan malam Bello mai gaskiya ne mutanen garin ba su yadda chewa she yayi kisan ba. Bayan kwana daya kuma aka kama wadan da sukayi kisan.

SHARE

Comments

    NO COMMENT

Leave Your Comment

Sign up to continue.

Your email address will not be published. Required fields are marked.

Already a member?? Login