nowayobloggers

An Kirkiro Da Budurwar Roba Don Taimakawa Maza Marasa Aure Su Samu Biyan Bukatar Jima’i
Daga Habu Dan Sarki
Jaridar Daily Mail ta kasar Ingila ta fitar da wani rahoto game da nasarar da wani masanin kimiyya Dr. Santos ya samu ta kirkiro da wata budurwar roba da aka yi mata siffar cikakkiyar mace, domin debe wa maza masu bukata kewa da biya musu bukatar su ta sha’awa.
Wannan budurwa da yanzu haka ake ta rububinta a kasuwannin kasar Ingila masu harkar irin wadannan dabarun fasaha na Artificial Intelligence, an sanya mata suna Samantha.
Masanin da ya kirkiro da Samantha ya bayyana cewa, an yi mata tsari mai inganci kamar na kowacce mace da za ta iya daukar hankalin namiji, yayin da aka tsara mata kalamai na soyayya da iya kwantar da hankali da motsa sha’awa.
Sannan haka yanayin jikinta, an yi mata al’aura da namiji zai iya jin dadi da ita wajen samun biyan bukatar sa.
Hasashe ya nuna cewa nan da wasu shekaru masu zuwa hankalin mutane zai koma kan amfani da irin wadannan halittu na roba da za a rika amfani da su, don biyan bukatar rayuwa, sakamakon gazawa wajen samun kyakkyawar mu’amala tsakanin mace da namiji.

SHARE

Comments

    NO COMMENT

Leave Your Comment

Sign up to continue.

Your email address will not be published. Required fields are marked.

Already a member?? Login